Salon Amfani da Ƙissa a Wasu Rubutattun Waƙoƙin Siyasa

    Tsakure: 

    A wannan nazari za a yi ƙoƙarin fito da wasu ƙissoshin Alƙur’ani mai girma a taƙaice waɗanda wasu mawallafa rubutattun waƙoƙin siyasa suka naɗe su a cikin wasu baitocin waƙa. Sanin kowa ne cewa rubutattun waƙoƙin siyasa ana wallafa su ne don tallata jam’iyya ko ɗan takara ko ƙushe jam’iyyar hamayya ko wani abu makamancin waɗannan. Su waɗannan ƙissoshi da mawallafa waƙoƙin siyasa ke amfani da su na daga cikin salailan da suke amfani da su wajen isar da wani saƙo wanda ya yi daidai da abin da wani ɗan takara ya aikata ko magoya bayansa suka aikata don ya zama abin koyi idan wannan abin na ƙwarai ne, ko ya zama abin gujewa idan wannan abin mummuna ne..

    Fitilun Kalmomi: Salo, Ƙissa, Rubutattun Waƙoƙi, Waƙoƙin Siyasa

    Download the article:

    author/Hassan Muhammad

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages