Auren Dole da Ilolinsa: Sharhi a Kan Waƙar Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

    Tsakure: 

    Sunan maƙalar Auren Dole da Illolinsa: Sharhi a Kan Waƙar Samaila Abdullahi FircinKoko. An samar da maƙalar ta hanyar yin hira da marubucin waƙar da samun kwafin waƙar daga gare shi. Haka kuma an sami rerarrar waƙar ga MP3 da ke ɗauke da muryar mawallafin waƙar, aka saurara domin nazari da shirin fitowa da abubuwan da ake buƙatar kawowa a cikin maƙalar.Bayan an nazarci waƙar an fito da batutuwa masu yawa da suka shafi auren dole da suka haɗa da dalilan da suka sa iyaye na yi wa ‘ya’yansu auren dole da kuma illolinsa. Idan aka shiga maƙalar za a sami dukkan bayanai. An yi tunanin samar da maƙalar domin ta yi susa daidai wurin da ke ƙaiƙayi a matsayin gargaɗi ga wanda yayi wa ‘ya’yansa auren dole da ya daina, wanda bai riga yayi baya nisance shi, shi kuma wanda ke da niyyar yi ya fasa. An yi amfani da hanyar nazarin waƙa ta Farfesa Abdullahi Bayero Yahya da ke cikin littafinsa mai suna Jigon Nazarin Waƙa. An kawo sakamakon binciken da aka gano sanadiyyar rubuta wannan maƙala tare da shawarwari da za su taimaka don samun mafita daga matsalolin da auren dole ke jawo wa al’umma.

    Fitilun Kalmomi: Aure, Auren Dole, Ilolinsa, Sama’ila Abdullahi Fircin Koko

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.021

    Download the article:

    author/Ɗangambo, H.A. and  Mainasara, A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages