Barazanar Ɗabi’un Zamani ga Al’umma: Nazari Kan Jigon Waƙar Ɗabi’un Zamani Ta Imamu Sani Gaya

    Tsakure: 

    Yadda barazana da ɗabi'un zamani suka dabaibaye rayuwar al’ummar Hausawa a yau, babban ƙalubale ne da ya daɗe ana tattaunawa a kai, wanda marubuta waƙoƙin Hausa ba a bar su a baya ba wajen bayar da gudummawa a wannan vangare, a ƙoƙarinsu na isar da saƙon don kwalliya ta biya kuɗin sabulu. Hakan ce ta sa aka tsara wannan takarda ta hanyar nazartar waƙar “Ɗabi’un Zamani”, ta Malam Imamu Sani Gaya, don fito da wannan barazana da ɗabi’un zamani ke tattare da su don kamo bakin zaren; wanda wannan ita ce babbar manufar takardar. Hanyoyin da wannan takarda ta bi wajen cim ma manufarta sun haɗa da karantawa tare da nazarin baitocin waƙar wadda aka samo daga wani littafi mai suna Waƙoƙin Malam Imamu Sani Gaya (2018). Sai kuma tattaunawa da wasu jama’a don ƙara fahimtar ire-iren ɗabi’u waɗanda zamani ne ya kawo su. Dangane da ra’in bincike, wannan takarda, an yi amfani da ra’in Gudummawar Adabi ga Al’umma da kuma ra’in Ɗangambo (2007) don cim ma manufarta. A sakamakon gudanar da wannan bincike an fahimci cewa, marubuta waƙoƙi sun taka rawa wajen kakkave ire-iren waɗannan munanan ɗabi'u, da zamani ya kawo a cikin waƙoƙinsu. Sannan an gano cewa munanan ɗabi’u sun yi kaka-gida a zukatan jama’a waɗanda idan aka yi ƙoƙari wajen magance su, to za a samu tsaftatacciyar al’umma.

    Fitilun Kalmomi: Barazana, Ɗabi’un Zamani, Al’umma, Waƙar Ɗabiun Zamani, Imamu Sani Gaya

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.028

    Download the article:

    author/Ɗangambo, H.A. and  Mainasara, A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages