Gobir Rumbun Waƙoƙin Makaɗan Baka: Ibrahim Hassan Bagwashe Mashigin Waƙa (1985-)

    Tsakure: 

    An bibiyi rayuwar Malam Ibrahim Hassan Gobir, Bagwashe ne, wanda a bisa tsarin zahiranci ya zamanto matattari na rumbun wasu mabambantan matanonin waƙoƙi na makaɗan baka na Hausa. A falsafar Ibrahim Gobir dangane da waƙar baka, ya samar da guruf-guruf daban-daban a Manhajoji na sada zumunta waɗanda suka haɗa da Manhajar WhatsApp da ta FaceBook da ta Instagram da dai sauran makamantansu waɗanda ake amfani da salula da nau’o’in wayoyin hannu da Kwamfutoci da dai sauran dangoginsu. Misali a WhatsApp ya buɗe Guruf wanda ya kira Diwanin-Waƙoƙin-Baka inda yake da mabiya sama da ɗari biyu da tamanin (280 followers), yayin da a Instagram yana da mabiya kimanin ɗari shida da saba’in (670 followers). A waɗannan manhajoji ana isar da wasu waƙoƙi ko hotuna waɗanda makaɗan baka na Hausa suka aiwatar a daɗaɗɗen lokaci da a halin da muke a ciki. Waƙoƙin bakan nan na Hausa sun shafi waƙoƙin Sarakuna da na jamian mulki, da na yansiyasa da na sojoji da na attajirai da na maaikata da na Shaihunan Malamai da na mafarauta da na ‘yantauri da na dabbobi da na tsuntsaye da na da na sauran masu sana’o’i da na gulabe da na garuruwa da da na sauran al’umma. Ta haka ne mabiya waɗannan guruf-guruf suke isar da saƙonnin tambayoyi dangane da wasu muhallai waɗanda sukan shige musu duhu a zubi na layuka ko ɗiya na matanonin waƙoƙin baka. Sau da yawa ma, sukan nemi bayanai game ko fashin baƙi na wasu ƙanana ko manyan maanoni ko manufofi na furucin matanoni na waƙoƙin baka. Haka kuma a kan kawo sunaye da tarihin rayuwa da hotuna na wasu makaɗan Hausa, marigaya da rayayyu, tsofaffi da manya da matasa da yara, maza ne ko mata, daɗa shahararru ne ko fitattu ko masu tasowa. Sannan akan kawo wasu kayan tarihi da na al’adu waɗanda suke jejjefo su a cikin matanoni na waƙoƙinsu da hotuna na wasu makaɗan baka. Sukan gabatar da kacici-kacici, musamman kan tarihin rayuwar wasu Sarakuna na Gobir da na wasu Sarakuna a Ƙasar Hausa.

    Fitilun Kalmomi: Gobirawa, Makaɗan Baka, Ibrahim Hassan Bagwashe


    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.005

    Download the article:

    author/Sa’idu Muhammad Gusau

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages