Tsakure:
Waƙa a siyasa kamar gishiri ne a cikin miya, rukuni ne kuma ginshiƙi ne babba a cikin harkokin siyasa, kusan a iya cewa, siyasa ba ta zama da ƙafafunta ba tare da waƙa ba (Usman 2013:3). Jam’iyyun siyasa sukan yi amfani da waƙoƙi domin yin kamfe, wanda a cikinsu ne suke bayyana manufofinsu da yin suka, da kawo hanyoyin gyara ko yin zambo har ma da zagi ga abokan hamayya ko tsakanin jam’iyyu biyu (Adamu 2003:54). Ta ɗaya hannun kuma akan sami waƙoƙi masu yin ɓatanci ga wata jam’iyya ko magoya bayan jam’iyya wani lokaci har da cin mutunci da zagi da yin fito-na-fito da zambo ta yadda manufar ta kauce hanyar hamayya ta zama adawa. A siyasance kalmar “Hamayya” ya kamata a yi amfani da ita wadda ba ta hana jituwa tsakanin ‘yan siyasa. Ba Kalmar “Adawa” ba mai manufar ƙiyayya ta har abada. Manufar wannan takarda ce, ƙoƙarin kawo manufofi na adawa maimaikon hamayya kamar yadda aka tsinkayi hakan a cikin wasu waƙoƙin siyasa a ƙasar Hausa domin faɗakarwa.
Fitilun Kalmomi: Hamayya, Adawa, Waƙoƙi, Siyasa, Ƙasar Hausa