Harshe Makamin Siyasa: Nazarin Yabo da Suka cikin Waƙoƙin Siyasa

    Tsakure

    Harshe yana ɗaya daga cikin tarin baiwar da Allah (S.W.T) ya hore wa ɗan Adam, wanda ake amfani da shi wajen sadarwa musamman ta hanyar yin magana ko waƙa ko hira da dai sauransu. Harshe yana daga cikin muhimman abubuwan da ake amfani da su a fagen siyasa, wanda hakan yakan taimaka wurin samun nasara ko akasin haka. Mawaƙan siyasa da dama sukan yi amfani da irin baiwar da Allah ya ba su na iya sarrafa kalmomi a waƙe wajen yabon jam’iyyarsu ko ‘ya’yanta, domin ɗaga su da tallata su ga sauran jama’a. Haka kuma da irin wannan baiwar ce suke amfani wajen sukar ‘yan adawa da jam’iyyar adawar domin dusashe haskensu. Wannan takarda ta yi nazarin yadda ake amfani da waƙoƙin siyasa wajen yabon jam’iyya da shugabanninta da kuma ƙoƙarin daƙushe hasken jam’iyyar adawa da magoya bayanta. A ƙarshe binciken ya gano cewa harshe wani ginshiƙi ne wajen tafiyar da al’amuran siyasa domin da shi ne ake tallata jam’iyya ko ɗan takara har su karɓu ga jama’a, kuma da shi ne ake kushe su ta hanyar suka wanda hakan kan rage musu farin jini ko ya janyo su rasa magoya baya. A cikin nazarin an riƙa kawo misalai daga baitocin waƙoƙin siyasa domin kafa hujja. 

    Fitilun Kalmomi: Harshe, Siyasa, Yabo, Suka da Waƙa

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.070

    Download the article:

    author/Jibril Yusuf

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages