Ƙididdigar Wakilin Suna a Waƙar Ta’aziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa

    Tsakure: 

    Wakilin suna yana ɗaya daga cikin muhimman rukunnan nahawu, don kusan duk zancen da za a yi a rubuce ko a baka, sai an samu ɗaya daga cikin nau’o’insa. Don haka, manufar wannan takarda ita ce ta ƙididdige nauoi da kuma yawa ko adadin wakilan sunayen da suke cikin waƙar Taaziyya ga Alhazan Nijeriya ta Nasiru Jikan Sarki Agadasawa. An gudanar da wannan nazari ta hanyar karanta waƙar domin fito da yawan nauoi da kuma ƙididdige adadin wakilan sunayen da suke cikinta. Sannan kuma, an gabatar da sakamakon wannan takarda ta hanyar amfani da taswirar kara-tsaye (bar chart) wajen ƙididdige wakilan sunayen da ke cikin waƙar. Takardar ta gano yadda marubucin waƙar ya yi amfani da wakilan sunaye guda casain da huɗu wajen isar da saƙon da waƙarsa take ɗauke da shi. Binciken ya nuna cewa marubucin waƙar ya ambaci nauin wakilin suna rakaɓau sau 23 a waƙar tasa. Sannan ya ambaci wakilin suna zagin aikatau sau (45). Ya kuma ambaci wakilin suna mallakau sau 15. Har wa yau, marubucin ya ambaci wakilin suna dogarau sau 4, haka shi ma wakilin suna gama-gari ya ambae shi sau 4a cikin waƙarsa. Har ila yau, marubucin ya yi amfani da wakilin suna nunau sau 2. Daga ƙarshe kuma, marubucin ya yi amfani da wakilin suna kaikaitau sau 1 rak a cikin waƙar tasa..

    Fitilun Kalmomi: Ƙididdiga, Wakilin Suna, Waƙar Taaziyya ga Alhazan Nijeriya, Nasiru Jikan Sarki Agadasawa

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.058

    Download the article:

    author/Sani Hassan & Nuhu Nalado

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages