Tsakure:
Tattaunawa a kan abin da ya shafi ‘kalma’, batu ne wanda manyan malamai suka fi yin magana a kan sa. Daga ciki akwai Aronoff (1976) da Bauer (1983) da Katamba (1994) da Haspelmath (2011). A Hausa ma, malamai ba su ba batun wata kulawa ba. A taƙaice, wannan maƙala za ta mayar da hankali ne a kan ‘kalma’ kawai, don cike wannan giɓi. Da farko an fara da kawo ma’anarta wadda aka fi amfani da mizani na zahiri wajen bayyana ma’anarta da nau’o’inta da matsayinta da siffofin kalma a Hausa da kuma yadda ake nazarin ta. Sakamakon wannan nazari ya fito da ma’anar kalma da nau’o’inta da matsayinta da siffofin kalma a Hausa da kuma yadda ake nazarin ta.
Fitilun Kalmomi: kalma, ma’anarta, nau’o’inta, matsayinta, siffofinta
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.023
author/Muhammad, I.A. and Umar, M.M.
journal/GNSWH, April 2024