Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makaɗa Bala Ganɗo ga Shugabannin Zamani

    Tsakure: 

    Sunan wannan maƙala shi ne, ‘Kukan Talaka Rabonsa: Muryar Makaɗa Bala Ganɗo Ga Shugabannin Zamani. An shirya wannan maƙala ce domin a yi nazarin muryar Bala Ganɗo a cikin wata shahararriyar waƙarsa mai suna, “Ba A Gane Manya Sai Ci Ya Samu”’don a fito da kokawarsa ga wani haƙƙi da aka hana masa. Ita waƙa hanya ce ta bayyana kai da isar saƙonni masu yawa ga jama’a. An zaɓi a yi nazarin wannan waƙar ce saboda kasancewarta mai ɗauke da muhimman bayanai da ke nusar da shugabanni ga irin halin da talaka yake tsintar kansa a duk lokacin da aka hana masa wani rabo da ya dace ya samu. An yi amfani da dabarar kawo ɗiyan waƙoƙin da aka tsinci wata magana mai muhimmanci da kuma kusanci ga shugabanni, sannan aka yi sharhi gwargwado. An ɗora Ra’in Mazhabar Gudummuwar Adabi Ga Al’umma (Psychoanalytical Theory) na Gusau (2015) a kan wannan maƙala. A ƙarshe, wannan takarda ta gano wasu zantuka da talaka yake furtawa a duk lokacin da wani ya hana ya sami rabonsa. Daga cikin ire-iren zantukan da aka gano akwai: ‘Bakin da Allah ya tsaga…’, da ‘kura da shan bugu’ da ‘arziki sai Allah’ da ‘kifi na ganin ka mai jar koma’ da sauransu. Makaɗa Bala Ganɗo ba kanwar lasa ba ne wajen isar da saƙon talaka ta wannan fuska a cikin waƙoƙinsa.

    Fitilun Kalmomi: Kuka, Talaka, rabo, murya, shugaba da zamani

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.015

    Download the article:

    author/Bunza, U.A. and Faruk , A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages