Tsakure:
Mata sun daɗe a harakar adabi, hasali ma da su aka fara, da su aka ci gaba da yi, kuma har yanzu da su ake yi. Mata sun fara rubutu tun lokacin Shehu Ɗanfodiyo, watau 1820, lokacin da Nana Asma’u ‘yar Shehu take rubutu a kan abubuwan da suka shafi addini. Daga cikin rubutunta akwai waƙa wadda ta rubuta a cikin harsunan Larabci da Fulatanci da Ajamin Hausa. Ko a wannan lokaci ta yi waƙe a kan abubuwa da dama, kama daga wa’azi da faɗakarwa da bege da jan hankali zuwa ga al’ummar musulmi musamman ga mata ‘yan uwanta. Don haka, rubutun waƙa ga mata ba sabon abu ba ne yana da daɗaɗɗen tarihi. Bayan su Nana Asma’u, mata sun ci gaba da rubuta waƙoƙi a kan fannonin rayuwa daban daban, kuma a ciki sukan mayar da hankalinsu a kan matsayi da matsalolin mata da al’amurransu tare da yin gargaɗi da faɗakarwa ga jinsin nasu na mata. Wannan muƙala mai taken Matsayi da Matsalolin Rayuwar Mata: Nazari Daga Rubutattun Waƙoƙi na Mata, ta yi nazari ne a kan yadda mata masu rubuta waƙa ke fitowa da irin matsayi da matsalolin da mata ‘yan uwansu ke fuskanta a cikin rubutattun waƙoƙin nasu. An kawo tarihin rubutun waƙa ga mata da matsayin da suke ba jinsinsu na mata da kuma matsalolin mata na rayuwa waɗanda mata ne kaɗai suka san su sosai, kuma su ke iya fito da su. Dukkan misalan da aka kawo daga rubutattun waƙoƙin da mata suka rubuta ne. Daga ƙarshe an gano cewa mata suna fito da mata a matsayin masu daraja da mutunci har dai in sun kama kansu, kuma sun dage da yin sana’a da neman ilimi da neman na kai wanda zai sa su yi mutunci ga idon mutane. An kawo shawarwari a kan yadda za a inganta rubutun mata na waƙa, a fito da su a kuma yi nazarin su a makarantu da wajen tarukan ƙara wa juna sani, don su samu karɓuwa kamar takwarorin su maza.
Fitilun Kalmomi: matsayi, matsaloli, rayuwar mata, rubutattun waƙoƙiauthor/Hadiza Salihu Koko
journal/GNSWH, April 2024