Tsakure:
Wannan bincike mai taken 'Salon Kamance A Cikin Waƙoƙin Bawa Namiji Jega'. Manufarsa ita ce nazarin waƙoƙin Bawa Namiji Jega don a fito da irin baiwa da hikimomin da Allah ya ba shi waɗanda yake amfani da su wajen shirya waƙoƙinsa. An bi hanyoyi guda biyu wajen tattara binciken, wato yin hira da mawaƙin da kuma nazarin waƙoƙin. Bayan nazarin waƙoƙin sakamakon ya nuna lallai akwai salailai na kamance a cikin waƙoƙin, wanda ya rabu gida uku, wato salon kamancen fifiko, salon kamancen daidaito da kuma salon kamancen kasawa, an yi sharhin salon da rabe-rabensa a cikin waƙoƙin.
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.038
Fitilun Kalmomi: Bawa Namiji Jega, Baiwa, Hikima, Shirya Waƙa, Salailan Kamance
author/ Abbas Musa
journal/GNSWH, April 2024