Tsakure
Makaɗan baka na Hausa kan yi amfani da hikima, da basirar da Allah ya yi musu wajen tsara maganganun, da za su ja hankalin mai sauraro ta hanyar amfani da adon harshe. Maryam Sale Fantimoti na ɗaya daga makaɗan da Allah ya horewa wannan baiwa, da hikima da zalaƙar zance. A wannan nazari an kalli yadda Maryam Sale Fantimoti ta yi amfani da dabaran adon harshe ta salon tsattsafi a wasu daga cikin waƙoƙinta. An ɗora binciken bisa ra’in ƙaye (Aethtetic theory). Dabaru da hanyoyin da ake bi wajen gudanar da wannan nazari sun haɗa da, tattaunawa da Maryam Sale Fantimoti da wasu masana. Binciken ya gano Maryam Sale Fantimoti tana amfani da tsattsafin haliyya wanda kan haifar da raha da soyayya da farin ciki da baƙin ciki, da sauran halaye da mutane kan tsinci kan su a ciki, dukkanninsu a cikin waƙoƙin nata. Manufar wannan takarda ita ce, jawo hankalin ɗalibai ‘yan’uwana da manazarta da ma masu sha’awar sauraron makaɗan, da su gane irin tarin hikimomi da fasahohin da ke ɗamfare cikin waƙoƙin makaɗa da mawaƙa. Hakan zai fito da irin gudummawar da suke bayarwa, musamman ga harshen Hausa, ta fuskar nuna ƙwarewa da gwanintar harshe. Wannan nazari ya kaɗaita a kan salon tattsafin haliyya ne kawai. Bincike zai ba da gudummawa wajen haskawa sauran manazarta da ɗalibai yadda za su fahimci adon harshen tattasafi a cikin ire-iren waƙoƙin situdiyo na Hausa.
Fitilun Kalmomi: Salo, Tsattsafi, Waƙoƙi, Maryam Sale Fantimoti
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.067
author/Samira Lawan Aliyu
journal/GNSWH, April 2024