Tsakure: Manufar takardar ita ce yin nazari a kan waƙar Annobar Korona da hanyar yi wa waƙar filla-filla ta amfani da hanyoyin nazarin rubutattun waƙoƙin Hausa domin a bayyana muhimman ɓangarori da nazari ya dogara da su, kuma masana suka amince a yi nazarin kowace rubutacciyar waƙa da waɗannan hanyoyin. Da yake nazari ne a kan rubutacciyar waƙa, an karanta waƙar (Annobar Korona) sosai ta yadda aka iya fayyace waɗannan muhimman ɓangarorin nazari, sannan aka kafa hujjoji daga baitocin waƙar. A sakamakon binciken takardar an gano cewa waƙar tana ɗauke da turke ko jigon faɗakarwa a kan cutar Korona, kuma ta cancanci a yi nazarin ta domin ta hau matakin nazari da masana da manazarta na adabin Hausa suka amince kowace rubutacciyar waƙa ta hau kamar salsalar waƙar da tarihin marubuci da shekarar wallafa da jigon waƙar da warwarar jigo da salo da sarrafa harshe da dabarun jawo hankali da dai sauran hanyoyi yin tarke ko nazari. Don haka, an bayyana dukkannin hanyoyin tarke ko nazari a cikin waƙar, sannan aka kafa hujjoji daga baitocin waƙar..
Fitilun Kalmomi: Tarke, Faɗakarwa, Waƙar ‘Annobar Korona, Khalid Imam
DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.060
author/Karofi, I.A., Rabeh, H. and Darma, A.Y.
journal/GNSWH, April 2024