Tsattsafin Bandariya a Cikin Waƙar Zaura ta Sanin Balɗo

    Tsakure

    A waɗansu lokuta, makaɗa kan ɗauki wani abu a masa waƙa a bisa son ransu. Abin da za su yi wa waƙar yana iya zama abin mamaki ko takaici a gare su. Daga cikin ire-iren abubuwan da sukan ɗauka su tsara waƙa a kansa har da abin da ya shafi zamantakewa. A kan sami wani abu da ya yi wa mutum daɗi ko akasin haka wato rashin daɗi, ta yadda da zuciya ta bayar da rinjayenta a kansa, kwatsam sai a ji waƙa ta fito. Haka abin ya kasance ga wannan waƙa da aka yi nazarinta a cikin wannan maƙala, waƙar bazawara ta Sanin Balɗo. An nazarci waƙar aka kuma yi ƙoƙarin fahimtar dangantakar Sanin Balɗo da bazawara domin sanin yadda aka yi wannan waƙa ta fito har ta zama abar sha’awa take kuma bawa mutane dariya a duk lokacin da suka saurareta. Daga cikin ire-iren dariyar da aka hango a cikin waƙar sun haɗa da dariyar ƙeta da ta mamaki da sauransu. 

    Fitilun Kalmomi: Tsattsafi, Bandariya, Waƙar Zaura, Sanin Balɗo

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.066

    Download the article:

    author/Rabiʼatu Abubakar Umar

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages