Gabatarwa
1. Manazarta ai
nazari kan waƙa,
Domin nazari
kan ma’aunin waƙa,
Shi ne ginshiƙin
kimiyyar waƙa.
2. Ma’aunin waƙa shi
ke bambanta zube,
Idan ko an yo
taliyo har gobe,
Aruli shi ne
nahawunmu na waƙa.
3. Idan ko waƙa ta ƙi amsa
Aruli,
Tilas masana ku
ji wannan ƙauli,
Mafita dai gun
Malamanmu na waƙa.
4. Cikin biyu
dai dole a samo mafita,
A samo hujja
wadda ta inganta,
Na tantance ƙafafu
na wannan waƙa.
5. Marubucin waƙa ya
samar baiti,
Shi mai nazari
shi yake li’irabi,
Ya sanya ƙafafu
kan gaɓoɓin waƙa.
6. Idan sun karɓa sunyi kan-kan-kan to,
A dukka karorin
sun yi riga da gyauto,
Aruli ya
inganta wannan waƙa.
7. A dukka
karorin fa idan sun ƙi su hau,
Cikin biyu
tabbas ba guda wanda ya hau,
Ku ce musu
zance bai zame war waƙa.
8. Muna da
ma’auni kan zuwan Larabawa,
Arulinmu yana
nan na ‘yan Hausawa,
Da shi ne muka
tantance dukkan waƙa.
9. Saninsa
muhimmi ne ga duk mai nazari,
Ya gane waƙa
take, yanke sarari,
Shi ne ya
bambance Ƙur’ani da waƙa.
10. Kowane
ilimi na da amfaninsa,
Ka bar
ma’abutansa su je nazarinsa,
Ilimin ya zamto
ribaɗin waƙa.
11. Ga dukka
gudanmu wanda ya yi wakilci,
Mu mar son
barka ya tsare mana ‘yanci,
A kan wannan
fannin kimiyyar waƙa.
12. Idan kuma
ba ɗai a cikin
al’umma,
Da za yai
magana gwargwado ma dama,
A bisa Aruli
don kimiyyar waƙa.
13. Masana ku
fahimta da sauran aiki,
Ku faɗaɗa ilimi don ku kawo ɗauki,
A kan bigiren
nan na Arulin waƙa.
14. Masha Allah
yanzu kam mun dace,
‘Ya’yan Hausawa
a yau sun ƙwace,
Suke ta rubutun
Arulin waƙa.
15. Masana da
yawa sun wuce ai gwalo,
Irin su
Galadanci da Sheshi da Bello,
Sun yi rubutu
kan Arulin waƙa.
16. Magabata
sun yi rubutu da yawa,
Irin su ubana
Baba ɗan Dunfawa,
Da ya ba ni
karatun Arulin waƙa.
17. Don haka ne
na ɗauki alƙalamina,
In tofa ɗan albarkacin bakina,
Don in yi waƙaƙƙen
Arulin waƙa.
author/Alhaji Ibrahim
journal/GNSWH, April 2024