Yabo Fitilar Mawaƙa: Tsokaci Daga Waƙoƙin Siyasa na Alhaji Kamilu Dan Almajirin Mawaƙa Nguru

    Tsakure: 

    Muhimmancin marubuta waƙoƙin Hausa a cikin al’umma ya fi gaban a bayyana, mutane ne da Allah ya yi wa baiwa da basira da ilimin sanin yadda zasu isar da saƙo ga jama’a ta hanyar waƙoƙinsu. Don haka wannan aikin an raɗa masa suna da “Yabo Fitilar Mawaƙa: Tsokaci Daga Waƙoƙin Siyasa Na Alhaji Kamilu Ɗan Almajirin Mawaƙa Nguru.An yi ƙoƙarin nazarin yadda mawaƙin ya yi amfani da jigogin Yabo, a waƙoƙinsa na siyasa da aka nazarta. Binciken ya fito da jigogin yabo da yadda mawaƙin ya yi amfani da su domin isar da saƙoninsa, ga masu sauraro da kuma masu nazari. Dabarun da aka bi don gudanar da wannan aikin su ne, leƙa wasu Littattafai da Kundaye da kuma Maƙalu da suke da alaƙa da wannan aikin, haka kuma an tuntuɓi sha’irin dangane da waƙoƙinsa da aka yi amfani da su a wannan aikin. Manufar wannan aikin ne ya fito da hanyoyin da sha’irin yake bi, wajen yabon iyayen gidansa da ma jam’iyyar da ya ke yi wa waƙa. Aikin ya gano shairin ya yi amfani da kyawon hali, da jaruntaka, da riƙon amana, da asali,da kyauta, da iya mulki, da son jama’a,da kuma tausayi na gwanayen nasa wajen ya yaba musu.

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.037

    Fitilun Kalmomi: Yabo, Fitila, Mawaƙa, Waƙoƙi, Siyasa

    Download the article:

    author/Bashir, A.S., Halilu, S. and Sadiq, A.

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages