Yabon Nasaba a Waƙoƙin Narambaɗa: Dangoginta da Dangantakarsu da Wanda ake wa Waƙa

    Tsakure: 

    Yabo a cikin waƙoƙin baka shi ne danganta wasu halaye da ɗabi’u kyawawa ga wani domin masu sauraren waƙa su ga girmansa da ɗaukakarsa a cikin al’umma. Ana yin haka ne ta hanyar amfani da kalaman koɗawa ko kambamawa ko cicciɓawa domin tabbatar da abin da aka ambata game da shi ga masu sauraren waƙar. Yabo shi ne abin da Tsoho (2013:1) ya kira shi yabau. A cikin rabe-raben yabo (yabau) da ya kawo akwai yabon dangantaka (nasaba), a wajen da ya nuna ana yaba mutum ta hanyar danganta shi da iyaye da ‘ya’ya da mata da ‘yan uwa da abokai da abokan arziki da barwa da sauransu Tsoho (2002:171-195). Irin wannan yabon na dangantaka (nasaba) shi ne maƙalar ke son ta duba a cikin waƙoƙin Ibrahim Narambaɗa domin fitowa da matsayin waɗanda aka danganta wanda ake yabo da su.

    DOI: 10.36349/djhs.2024.v03i01.011

    Fitilun Kalmomi: Yabo, Waƙoƙin Baka, Ibrahim Narambaɗa

    Download the article:

    author/Atiku Ahmad Dunfawa

    journal/GNSWH, April 2024

    Pages